Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u
Kwankwaso, ya ce ba zai mayar da martani ga
shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ba a kan
zargin da ya yi cewa shi [Kwankwaso] ya kwashe
kudin jihar ya yi yakin neman zabe a shekarar
2015.
Sanata Kwankwaso ya ce "ba zan ce komai a kan
wannan zargi ba saboda shugaban kasa bai san
komai a kan yarda muka tafiyar da mulki a Kano
ba."
Dan majalisar dattawan ya bayyana haka ne a wata
hira ta musamman da aka yi da shi a gidan rediyon
Dala FM da ke jihar ta Kano ranar Talata da
daddare.
Kwanakin baya ne lokacin da Shugaba Buhari ke
ziyarar aiki a kasar Faransa, ya shaida wa wani
taron 'yan Najeriya, ciki har da 'yan jihar Kano, cewa
gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kammala
ayyukan da mutumin da ya gada, Sanata
Kwankwaso ya bari bayan da ya kwashe kudin jihar
ya yi yakin neman zaben shugaban kasa a 2015.
Kwankwaso da Buhari na cikin mutanen da suka
nemi tsayawa takara a jam'iyyar APC a wancan
lokacin, amma Janar Buhari ya samu nasara.
Me ya sa Buhari 'ya hana Kwankwaso sakat'?
Buhari ya yi wa su Kwankwaso fatan alheri
"Mutane da yawa sun zo sun gaya min abin da
shugaban kasa ya fada. Har bidiyon kalaman da ya
yi suka kawo mini. Abin da ya sa ba zan ba shi
amsa ba shi ne, ya yi maganganunsa ne kawai
wadanda ya ji daga wurin mutanen da ke kewaye
da shi. Bai san komai a Kano ba," in ji Sanata
Kwankwaso.
Ya kara da cewa Gwamna Ganduje bai ci gaba da
ayyukan da ya fara ba, yana mai cewa "dukkan
ayyukan da ya ci gaba da aiwatarwa "na gwamnatin
Shekarau abokin Buhari ne."
A cewar Sanata Kwankwaso, duk mutanen da ke
zuga shugaban kasa domin ya bata masa suna ba
sa kaunarsa.
Ya ce "sun je suna gaya masa cewa ni dan ta'adda
ne, ba na son Buhari. Amma ina so ku sani cewa
duk cikin wadannan mutane ba wanda yake son
Buhari kamar ni domin ni na taimake shi [ya ci
zabe].
Ganduje makiyi ne
A karon farko tsohon gwamnan na jihar Kano ya yi
tsokaci kan bidiyon da ke zargin gwamna Ganduje
da karbar cin hanci na dalolin Amurka.
A cewar sa, "Kafin a fitar da bidiyon na samu labari,
amma na ce kar su sake shi. saboda abin kunyar
ba kawai na iyalin gwamna ba ne, abu ne da ya
shafi martabar mutanen Kano da addininsu da
kuma kujerar da na rike mai alheri."
Sanata Kwankwaso ya ce dukkan mutanen Kano sun
zama abubuwan kyama a idanun duniya saboda
abin da ake zargin gwamnan jihar da aikatawa.
Ya ce gwamna Ganduje masoyinsa ne wanda ya
rikida ya koma makiyi.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya sha alwashin yin
aiki tukuru wajen ganin an sauya "wannan gwamnati
rubabbiya."
Ya ce ayyukan da dan takarar gwamna na jam'iyyar
PDP, Alhaji Abba Kabir ya yi a lokuta daban-daban
za su ba shi damar yin nasara a zaben 2019.
Please idan kun karanta kudinga sharing
No comments:
Write Comments