Google Mail wanda akafi sani da gmail zamu iyacewa shine email da akafi amfani dashi a duniyar yanar-gizo, saboda yanada tsare-tsare dadama.
Google Mail yanada amfani sosai domin akwai abubuwa da dama akeyi dashi wanda babu dama ayi dawasu email din, da Google Mail zaka iya samun kudi ta yanar-gizo, amma nasan wannan damar bakowa bane zaigane sai wanda yake harkar internet sosai.
Google Mail yanada tsaro sosai fiyeda sauran email, shiyasama mutanen duniya masu amfani da yanar-gizo suke aiki dashi aharkokinsu na yau da kullum, na yanar-gizo.
Google Mail yanada matukar sauki wajen aikewa da karban sakonni. Kuma duk wani abu na kamfanin google zaka iyayi dashi saboda shi mallakin kamfanin google ne.
Da Google Mail ake bude channel a YouTube, channel shine wani guri ko wani shafi da ake budewa a YouTube domin ana daura bidiyo, wasu kuma suzo sukalli wannan bidiyon.
Abubuwan Da Ake Bukata
Lambar waya.
Browser kamar "Chrome".
Kakaranta wannan darasin gaba-daya.
Ga Yanda Akeyi
Dafarko, kabude browserka, sannan karubuta "www.gmail.com" acikin gurin saka adreshi na browserka, saika kadanna "GO" kokuma "OK" awasu browser. Bayan tagama bude maka shafin, saikayi kasa kashiga "Create New Account".
Daganan zata kawoka gurinda zakayi rajistar sabon adreshin email naka na kamfanin google kokuma ace gmail. Karkashin "Name", wato suna, kawai kasa sunanka kadai, banda sunan mahaifi, wato wajen yin rubutu nafarko kenan,
Misali "Nura" amma, anaso kayi amfani da suna maikyau.
Sannan saikasa sunan mahaifinka, banda sunanka, agurin yin rubutu na biyu.
Misali "Mahdi" nanma anaso kasa suna maikyau, kokuma wani sunanda bazaka mantaba.
Yanzu kuma, saikasa sunan dakakeso yazama shine adreshin gmail naka acikin inda aka rubuta "Choose your username".
Misali "nuramahdi". Nan kuma yanada kyau kasa sunan dazai zamanto akwai bambanci, saboda idan akwai wani mai wannan sunan, bazaka iya amfani da wannan sunanba, dolene kasa suna na musamman, wanda babu irinshi.
Saikuma kasa "Password" wato lambobin sirri, a inda aka rubuta "Create a password".
Misali kasa "@@mypass$!". Yanda kyau kasa "Password" mai karfi wanda wani bazai iya ganewaba, sai kai kadai. Ina baka shawara kasa harufa, da lambobi, dakuma alamomin rubutu wato "Symbols" acikin lambobinka na sirri, kamar yanda nayi misali asama.
Sannan kasake saka lambobin sirrin dakazaba acikin inda aka rubuta "Confirm your password".
Misali "@@mypass$!". Ammafa kasani dolene lambobin sirrin dakasa agurin na sama shi zakasa agurin kasanma, dolene dukkansu biyun suzamanto iri daya.
Wajen "Birthday" kuma, saikazabi watan da aka aifeka, misali "February" wata nabiyu kenan.
Sannan kuma kazabi nawagata aka aifeka, misali "2" wato biyu ga wata kenan.
Sannan kuma saikazabi awace shekara aka aifeka, misali "1995".
Sannan karkashin "Gender", wato jinsi, kazabi jinsinka, misali kazabi "Male" idan kai namijine, idan kuma mace ce saita zabi "Female" wato mace a matsayin jinsinta.
Saikuma wajen "Mobile phone", wato lambar waya, kazabi kasarka, nide dan "Nigeria" ne, saboda haka nazabi "Nigeria" amatsayin kasata. To kaga kenan kaima saika zabi kasarka, kokuma daga kasarda kakeyin browsing daga can.
Daganan suda kansu zasu sakama "Country code" nakasarka, wato code na layin sadarwar kasarka, kokuma kasarda kakeyin browsing daga can. "Country code" na "Nigeria" shine "+234", yana dakyau kasani cewa kowace kasa "Country code" nata dabanne, dana wata kasa.
Yanzu kuma saika saka lambar wayarka ita kadai, misali "08012345678". Ammafa anan dole kasa lambar wayar datake aiki, domin zasu iya tuntubarka, nan take, dan sutabbatar dacewa kaine.
Karkashin "Location" kuma, kazabi kasarka, amma mafi yawanci de suda kansu zasu zabamaka kasarka. Nide daga "Nigeria" nake saboda haka sun sakamun "Nigeria" amatsayin kasata. Saboda haka kaima sai ka zabi kasarka, kokuma kabari suda kansu zasu zabamaka.
Bayan kagama, duk abunda mukace kayi asama to kayi kasa kadanna "Continue".
Yanzu, kuma danna wannan shudin madannin(Blue button) wanda yanuna kasa, saikayita dannashi, har sai yanuna "Combining data". Sannan sai kadanna inda aka rubuta "I AGREE".
Daganan zata kaika wajen dazasuyi maka barka da zuwa, wato Welcome, saikayi kasa kashiga inda aka rubuta "Continue" tareda sunanka.
Bayan kagama komai zasu kaika cikin inbox naka, na sabon adreshin gmail daka bude yanzu.
Yanadakyau idan kazabi suna ko adreshin email, idan sukace akwai mai wannan sunan to kakara wasu lambobi. Misali kazabi nuramahdi idan akwai mai wannan sunan sai kakara wasu lambobi kamar nuramahdi223 kuma gurin lambobin sirrin kasa alamomin rubutu wato Symbols, saboda yanzu akwai mutanen da suke mugunta suna kwacewa mutane email nasu, amma idan kasa lambbobin sirri mai wahala gane to zaka samu tsaro kenan.
Yanadakyau bayan kagama bude sabon adreshin gmail, kabude kaje kasa Recovery email. Recovery email shine wani email dazaka saka koda wannan email din naka yasamu matsala zaka iyaseta komai ta hanyar amfani da shi.
Sannan akwai Recovery number, nan shima duk lambar dakasa da ita zakayi amfani wajen dawoda account naka koda kamanta password ne.
Nan shine karshe wannan darasin, kuma kuna iya temaka mana, ta duk inda kukaga munyi kuskure, kokuma munyi wani abunda kuke ganin, baidace ace munsa a wannan shafinba, kuma kuna iya turomana naku labarin, domin mukaru dukkanmu, wasuma sukaru daku, damu baki daya, haka shine agudu tare atsira tare.
Sannan karkuma manta, kuna iya ajiye comment naku, a wajen comment da aka kebe akarkashin kowane darasi, dakuka karanta a wannan shafin. Sannan muna bukatar kutemaka kutura wannan darasin ga 'yan uwa, da abokan arziki, kota dandalin sada zumunta na Whatsapp, Twitter, Facebook, Instagram dasauransu. Mungode, sai mun hadu a darasi nagaba,
No comments:
Write Comments