Need To Contact Me :- +2349021664821

Saturday, May 12, 2018

Home Wai Shin Menene Email Address ? Meye amfaninsa Shiga ku Karanta zaimuku Amfani

Subscribe Our Channel


tw
image ©
Assalamu alaikum, ma'abota da masu karatu a wannan shafin, muna fatan kowa yana lafiya.


Mutane dayawa, sukan tambayemu, cewa wai shin menene Email?. Kuma menene banbancin Email da Gmail ne?



Yau acikin wannan darasin, zamuyi muku bayanin menene Email?, sannan kuma menene Gmail?, daga baya kuma, mu bambance menene Email da Gmail.



Dafarko Menene E-mail?

Kalmar E-mail a turance, tana nufin "Electronic Mail" wato hanyar turawa, dakuma karban sakonni, ta yanar-gizo, kokuma ta hanyar amfani da na'urorin laturoni. Kuma hanyace maisauki da zaka iya tura sakonni, kuma kaima za'a iya aikomaka sakonni. Sannan shi E-mail yanada muhimmaci sosai a wannan lokacin, kuma kusan duk wani ayyukan gwamnanti da kuma harkokinta na internet dasauransu.



Menene Gmail?

Gmail shima hanyace da ake tura sakonni ta yanar-gizo. Idan akace Gmail to bashida banbanci da E-mail.



Bambancin Gmail Da Email

- Idan akace E-mail, to ana nufin wata hanyace da'ake tura sakonni ta yanar-gizo, acikin sauki, kuma akyauta.



- Kamar yanda mukasani, akwai kamfanonin layukan sadarwa(Sim Card) dayawa, kuma daban-daban, misali akwai 9mobile, Airtel, MTN, dasauransu.



- Sannan kuma munsan cewa duk abunda MTN, zaiyi to suma Airtel, da 9mobile zasuyi. Suma haka E-mail. Shi idan akace E-mail kamar ance Sim Card ne, idan kace Sim Card kaga baka banbance wane Sim card na wane kamfani ba, amma idan kace Sim na MTN kaga kawai kace layin MTN. To shima idan akace Gmail kana ana nufin E-mail, amma na kamfanin Google ne.



Nau'ukan Email

Dayawa anfi sanin wa'annan.

- Google Mail(@gmail)


- Yahoo Mail(@yahoo)


- Hot Mail(@hotmail)



Akwai kamfanonin dasuke bada damar abude addreshin email akyauta, kuma suna dayawa, ammade anfi sanin guda ukun nan damuka baiyana asama, sannan kuma acikinsu gaskiya @gmail yafisu tsaro, dakuma dadin sha'ani.



Kuma, zaka iya bude adreshin email, naka nakanka akyauta, sannan idan zaka bude kawai lambar wayarka zakasa, sanna kacike sauran bayanai.



Email ana amfani dashi a zamanin nan, domin bude asusun banki, sannan kuma ana tabbatar da wannan asusun dakabude ta hanyar email.



Idan mutum zainemi aiki awasu kasashen, zakaga ance masa dolene yasaka email nashi, domin tanan zasuna tura masa duk wasu sakonni, da sanarwa, dakuma sauran labari.



Ta email zaka iya tura sakon bidiyo, hotuna, ko sautin murya cikin sauki. Kuma email bashida wahalar aiki, saide wasu mutane dadama, sukanyi asarar datarsu wajen aiki da email, saboda rashi kwarewa wajen aiki da email din.



Bayanin Karshe

Email da Gmail duk abu dayane, basuda bambanci. Sannan kuma akwai kamfanoni dasuke bada damar mallakan email daban-daban, ana iya amfani da email, aduk wata waya datakeda internet, ammade yafi dadin aiki, akan manyan wayoyi da na'urorin kwamfuta.



Mafi yawa, kamfanonin dasuke bada damar amallaki adreshin email, mallakin turawane, kuma akwai dokoki da ka'idojin aiki dasu, saboda haka yanada kyau akiyaye dokokin dasukasa, domin karya doka, yana iyasa sukullemaka adreshin ka na email.



Nan shine karshen wannan darasin, dafatan wannan darasin zai temaka, wajen gane email, dakuma amfaninshi, sannan kuma kasan cewa email, da gmail, dan jumane, da dan jummai.



Muna bukatar katura wannan darasin, zuwaga yan uwa, da abokan arziki, domin suma su karanta sukaru, muma mukaru gaba daya. Mungode, sai anjima, kuhuta lafiya.

1 comment:
Write Comments