Assalamu alaikum, ma'abota da masu karatu a wannan shafin, muna fatan kowa yana lafiya.
Website komuce shafi a yanar-gizo, yana nufin wani shafi, kokuma wani gurin da mutum zai iya kai ziyara a yanar-gizo, domin ya karanta wani abu, kokuma yasaukar wato downloading nawani abu, ko kuma yatallata(advertisement) kayanshi, kokuma yasiya abubuwa acan wanda ake kira Online Market.
Ana gina website ne domin baiwa masu kawo ziyara, damar samun karuwa da abunda akasaka acikinshi, kokuma abunda shafin yakunsa, sannan kuma shi maikai ziyara, zai iya samun damar da zaiyi amfani da abunda aka saka acikin shafin akyauta, amma awasu shafukan sai anbiya kudi.
Ana gina website ne domin hada kan al'umma daga gurare daban-daban a fadin duniya, wanda akafi sani da Social Media.
Meyasa Ake Gina Website?
Ana gina website domin dalilai dadama, kokuma manufofi dadama, ga wasu daga cikinsu, dakuma muhimmancinsu ga jama'a baki-daya.
KAMFANI:
Kamfanoni suna gina shafi, komuce website, domin su tallata kayaiyakin dasuke kerawa, kokuma sukeyi ga ma'abota hajarsu, tahanyar yanar-gizo, ganin cewa awannan zamanin mafi yawan jama'a, sun koma amfani da internet wato yanar-gizo, a harkokinsu na yau da kullum, to da wannan dama kamfanoni a zamanin yanzu suke amfani sutallata hajarsu ga al'ummar duniya baki-daya a internet.
BANKI:
Bankuna suma ba'abarsu abayaba, domin suma awannan zamani suna amfani da shafin yanar-gizo, domin subawa amfani da bankunansu, damar musayar kudi, ta yanar-gizo, kokuma subawa mutane damar bude sabon asusun bankinsu akyauta, ta yanar-gizo. Hada-hadar kudi awannan zamani kusan takoma ta yanar-gizo, amma mafi yawa akasashen dasukaci gaba(Developed countries) ne.
GWAMNATI:
Gwamnatoci musamman akasashen dasuka cigaba, mafi yawanci aikace-aikacensu yakoma ta hanyar yanar-gizo, saboda awannan zamanin mutane sun maida harkokinsu kacokan a yanar-gizo, to da wannan dama gwamnatoci suke yada manufofinsu, da labaransu kokuma sutallata ayyuka ga yan kasa, masu amfani da yanar-gizo. A wasu kasashen hatta zabe(elections) ana iyayi ta hanyar internet saboda kawai sunci gaba, sannan kuma sunada isasshen tsaro a yanar-gizo.
LABARAI:
Kafafen yada labarai suna amfani da yanar-gizo domin su yada labaransu ga ma'abota yanar-gizo, sannan bugu da kari yada labarai ta yanar-gizo yanada banbanci da akwatin rediyo(Radio) saboda, a yanar-gizo ana iyasaka hoto domin karin haske gamai karanta labarin, amma a akwatin rediyo sai yaji murya, kuma ba'aganin hoto. A yanar-gizo kafafen yada labarai suna iyasaka labarai tareda hoton bidiyo ko sautin murya da mutum zai iya sauraro.
SIYASA:
Kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, dakuma karfin soja, kamarsu Amurka, Burtaniya, Faransa, Jamus, Jafan, Kasar Sin(China), Kanada, Rasha, Turkiya, Indiya dasauransu suna yada manufofinsu gameda siyasar duniya ta hanyar yanar-gizo, da sauran hanyoyin yada labarai, nazamani. Sannan kuma yan takara a matakin zabuka daba-daban, suna amfani da yanar-gizo domin yada manufofinsu, dakuma yakin neman zabe wato Campaign a wannan zamanin.
Nan yakamata mutsaya awannan darasin. Amma idan Allah yasa munada nisan kwana, zumucigaba daga inda mukatsaya wani lokacin agaba. Muna fatan wannan darasi zaiyi muku amfani, danganeda fasaha a wannan lokacin.
Nan shine karshe wannan darasi, kuma kuna iya temaka mana, duk inda kukaga munyi kuskure, kokuma munyi wani abunda kuke ganin, baidace ace munsa a wannan shafinba, kuma kuna iya turomana naku labarin, domin mukaru dukkanmu, wasuma sukaru daku, damu baki daya.
Sannan karkuma manta, kuna iya ajiye comment naku, a wajen comment da aka kebe akarkashin kowane darasi, dakuka karanta a wannan shafin. Sannan muna bukatar kutemaka kutura wannan darasin ga 'yan uwa, da abokan arziki, kota dandalin sada zumunta na Whatsapp, Twitter, Facebook, Instagram dasauransu. Mungode, sai mun hadu a darasi nagaba, kuhuta lafiya, sai anjima.
No comments:
Write Comments