Need To Contact Me :- +2349021664821

Saturday, May 12, 2018

Home Yadda Ake Rooting din Wayar Android

Subscribe Our Channel



image © Techtakecare_Com
KIMIYYA,
FASAHA
KOYAR WA
dadae duk abunda ya shafi internet dama Abubuwan da Ba a Net yakeba
To yau mun kawo muku yadda ake Rooting din waya da farko dae
Menene Rooting?

Rooting anayiwa wayoyine, musamman kirar Android domin subude wasu application dinda basa buduwa sai anyiwa waya rooting. Awasu wayoyi ma anayin irin wannan abun, misali a wayar symbian ana mata hacking domin yazamanto takara kokari akwai wasanni(Games), da wasu application dadama wanda idan ba'ayi hacking na symbian ba bazasuyi aiki akan wannan symbian ba. To ita hakane a wayar Android akwai abubuwa dadama dadole saikayi rooting na wayar sannan kasamu damar moresu.



Amfanin Rooting Ga Wayar Android

Rooting yana amfanine a waya, domin yabada dama wayarka tayi wani abunda idan ba'ayiwa wayar rooting ba, bazatayiba. Sannan kuma yana baka damar yin hacking na games kokuma application. Application kamarsu Screenrecoder da Flashify basa aiki harsai anyiwa waya rooting. Munyi darusa dadama awannan shafin, wa'anda idan bakayi rooting ba bazaka iyayinsuba, ammafa fa badole bane saikayi rooting na wayarkaba. Akwai wasu abubuwa dazaka gani idan kanayin game kokuma kana amfani dawasu application dole sai anbiya kudi kokuma ansamu coins dayawa kafin asamu damar yinsu. Idan kayi rooting kana iya hacking nasu kamoresu akyauta, kokuma batare da katara coins dayawaba.



Gaskiya nasha yin kokarin yiwa wayata rooting, amma nakasa dafarko, daga baya wani abokina yanunamun wannan hanyar kuma nayi naga yanayi sosai, saboda haka naga yadace nanuna muku ita, kuma kubita wannan hanyar domin rooting na wayarku.



Shi Dolene Sai Nayi Rooting?

Kasani badole bane sai kayiwa Android dinka rooting ba, kawai ganin damane, ammade akwai wasu abubuwa dadama da dole za'abukaci rooting. Koda bakayiwa wayarka rooting ba zatayi abubuwa dadama batare da matsalaba.




Abubuwan Da'ake Bukata

Saukar da KingRoot.apk

Kasaukar da Framaroot.apk

Kakaranta wannan darasin gabadaya.



Ga Yanda Akeyi

Dafarko ka saukarda wannan application din maisuna KingRoot.apk, saikayi installing nashi, bayan kagama installing nashi kawai kabudeshi, zakaga wani hoton kwado, kokuma dan makulli fari bayanshi kuma akwai wani koren(green colour) launi, to kawai kadanna kan wannan dan makullin, idan zakayi rooting nawayar taka.





Bari mufara rooting din kawai. Kadanna kan wannan kwadon domin kayiwa wayarka rooting, kana danna kanshi zakaga yafara kewayawa(rotation) to idan yafara haka yana nufin yafara rooting nawayar.





Bayan kagama da hanyoyin da muka nuna maka asama kawai, kadan jira kadan zatagama rooting din cikin minti daya(1 minute), dazarar tagama rooting din, zatasa alamar maki akan wannan gurin da kwadon yake. Wato hakan yana nufin kayi rooting na wayarka.





Wannan darasin nagwadashi awayata kirar Android maisuna Tecno H5. Kuma rooting yayi mata lafiya kalau, domin yanzu haka dashi nake aiki. Karin bayani wannan application din wato KingRoot.apk gaba daya nauyinsa shine 1.38MB kadai. Saideshi yana zuwane da yaren china, kuma yana aiki sosai fiyeda sauran abubuwan rooting na Android.



Idan kataba gwadayin rooting kuma wayar taki rooting, ga shawara kasaukarda wannan application din maisuna Framaroot.apk, sannan kagoge wancan rooting dinda kayi kokarin yi baiyiba, ta hanyar dazamu muna muku nangaba kadan acikin wannan darasin.



Ga Yanda Zakayi

Kasaukar da wannan application Framaroot.apk awayarka, sannan kayi installing nashi, bayan kagama installing nashi, saika budeshi, daga sama zakaga inda aka rubuta Install SuperSU, acikin wani guri(dropdown menu) kawai kashiga wannan gurin.





Kana shiga wannan gurin, zakaga wasu rubutu ajere(list) kusan uku ko hudu, kaduba sai zakaga Unroot kawai kadannan kanshi, acikin list dinda kagani kokuma suka nuna maka.





Daga nan sakayi kasa, kadanna inda aka rubuta Barahir.





Kana dannawa zata rubuta maka Unroot done!. Wato kagoge wancan rooting dinda kayi kokarin yi kenan dafarko. Shawara bayan kayi Unrooting nawayarka, wato kagoge rooting nawayarka, kayi uninstall na wannan application wato Framaroot.apk din.





To kana gama wannan saikaseyi mata rooting ta hanyar damuka nuna muku tafarko, wayarka zatayi rooting cikin sauki. Babu wata wahala domin kana iyayin rooting din acikin minti biyu.



Bayanin Karshe

Wannan hanyar itace mafi sauki wajen yin rooting na waya kirar Android, kuma babu wata wahala zaka iyayi acikin minti daya. Sannan kuma kana iya goge rooting(unrooting) nawayar taka idan kanaso, saboda bakowa bane yakeson yiwa wayarsa rooting ba. Ammade shawarata agareku, koda bakwasan rooting yana dakyau kusaka recovery mode awayarku, nan gama zaiyi muku amfani sosai.



Nan shine karshe wannan darasin, kuma kuna iya temaka mana, ta duk inda kukaga munyi kuskure, kokuma munsa wani abunda kuke ganin, baidace ace munsa a wannan shafinba, kokuma munyi wani darasi dakuke gani badede bane, kuna iyayi mana gyara,kuma kuna iya turomana naku labarin, domin mukaru dukkanmu, wasuma sukaru daku, damu baki daya.



Gamasu son sucanja version kokuma ROMs nawayarsu, kusani dolene saikuyi rooting nata. Kuma saika mata recovery mode, shikuma recovery mode ba'asakashi awaya sai anyi mata rooting. A baya mun bayanin yadda ake seta recovery mode awayar Android kuduba label na Android, zaku ganshi.



Sannan karkuma manta, kuna iya ajiye comment naku, a wajen comment da aka kebe akarkashin kowane darasi, dakuka karanta a wannan shafin. Sannan muna bukatar kutemaka kutura wannan darasin ga 'yan uwa, da abokan arziki, kota dandalin sada zumunta na Whatsapp, Twitter, Facebook, Instagram dasauransu. Mungode, sai mun hadu a darasi nagaba, kuhuta lafiya, sai anjima.

No comments:
Write Comments