na PDP, Atiku Abubakar watau,Peter Obi
ya gargadi 'yan Najeriya da cewa su guji
sake zabar gwamnatin shugaba Buhari
dan sake yin shekaru 4 akan mulki idan
ba haka ba wahala ba ta kareba. Peter Obin yayi wannan maganane a
jihar Legas wajan wani taro da ya
halarta jiya Asabat kamar yanda shafin
The Cable ya ruwaito, inda yace zabar
gwamnatin Buhari a karo na biyu na
nuna cewa kashin 'yan Najeriya ya bushe kenan domin tattalin arzikin kasar zai ci
gaba da tabarbarewane. Obi ya bayyana cewa, la'akari da kasafin
kudin shekarar 2019 da shugaba Buhari
ya gabatarwa majalisa za'a iya cewa
babu inda kasarnan zata je muddin
Buharin ya ci gaba da mulki. Yace kasafin kudin ya nuna cewa kashi
60 cikin dari za'a yi amfani da shine
wanjan biyan bashin da ake bin kasarnan
sannan kuma shi ya nuna cewa za'a tatsi
talaka dan a karbi haraji, yace Najeriya
fa itace kasa ta daya a Duniya a talauci to ta yaya zaga matsi wanda yake cikin
talauci kace zaka karbi haraji indai ba
karashi kake so ka yi ba? Obi yace, Bafa Buharine ke gudanar da
mulkin kasarnan ba kuma be damu da
yanda al'amura ke gudana ba. Yace idan aka zabesu zasu karfafawa
kanana da matsakaitan masana'antu
karfin gwiwa dan ganin tattalin arzikin
kasarnan ya habaka
No comments:
Write Comments