35 a duniya, wadda mazauniyar kauyen
Rafin-Makadi ce, a karamar hukumar
Rimi da ke jihar Katsina, ta shigar da
karar mijin ta Inusa Aliyu wajen 'yan
sanda, da laifin aikata fasikanci da 'yar su mai shekaru 14. Mariya ta tabbatar da wannan ta'asa da
mijin ta yake aikatawa bayan da ta
kama shi dumu-dumu a cikin laifi, inda
ta garzaya wajen 'yan sanda. Ta bayyanawa 'yan sanda cewa, daman
ta jima ta na zargin wannan abu, amma
gashi yau ta gani da idonta da dubu ta
cika kuma kuma daman ance gani ya
kori ji domin ya tabbatar ma ta da zargin
da ta jima ta na yi.
Mariya ta kara samun tabbaci daga
wajen 'yar ta su bayan da ta titsiye ta
akan sai ta fada mata a gaskiyar
lamarain inda ita kuma ba ta boye ma ta
komai ba.
Kakakin 'yan sandan jihar Katsina, DSP
Gambo Isah, ya tabbatar da cewa, Inusa
yana nan a hannun su domin cigaba da
bincike kafin su tura shi gaban alkali. Inusa ya amsa laifin da ake tuhumar shi
da shi, kuma ya ce wani dan duba ne ya
ba shi wani lakani kuma idan bai aikata
fasikanci da 'yar shi ba to kuwa lakanin
zai karye.
No comments:
Write Comments