Need To Contact Me :- +2349021664821

Friday, May 11, 2018

Home Applications Guda Goma 10 Da yakamata Duk Mai Amfanida Android Yasan Muhimmanci su

Subscribe Our Channel


tw
image © Techtakecare_Com

Akwai wasu applications dayawa, daya kamata ace duk wani mai aiki da manyan wayoyinda ake kira smartphone, yana aiki dasu saboda mahimmacin ga ita wayar kanta, dakuma shi mai aiki da wayar kanshi, kuma dukkansu basa bukatar rooting.



Wasu applications din, daga cikinsu ana aiki dasune, domin gyara wasu abubuwa kamar hoto da bidiyo. Wasu kuma aikinsu shine, su temakawa shi mai waya idan zanyi wasu ayyuka, da wayarshi, sannan kuma wajen gano wasu abubuwa.



Daga cikinsu akwai wanda explore ne, akwai kuma wanda kallon bidiyone nasu amfanin. Wasu kuma dole saida data, ake yin aiki dasu, wasu kuma basa bukatar akunna data, kafin ayi aiki dasu.



1. Google Chrome: Fast & Secure

Wannan ma browser ce kamar kowace browser, amma tana wasu aiyuka, wanda sauran browser basayi, kuma tana amfanine da Gmail tunda itanma kanta mallakin kamfanin Google ce. Akwai abubuwa masu yawa da akeyi da ita wanda sauran browsern basayi sai daddaya. Mutane dasuke harkar gina shafin yanar gizo wato wa'anda ake kira da Webmaster's, ko Blogger suna aiki da ita wajen yin harkokin na internet saboda idan ba wannan browser ba gaskiya sauran basayi saide daddaya. Masu bude shafin Blogger nasan sune zayi muku cikakken bayani gameda amfaninta, wandani anan bafadesuba saboda bangano suba, kumade ban san suba.



Amfaninta

Budewa da aikin Blogger.

Budewa da aikin WordPress.

Saurin browsing.

Bude kowane irin shafi.

Yin kallo online.

Sauraran audio a online.

Karfin browsing.

Destop version.

Ajiye password da username.

Hada PDF File.



2. Opera Mini

Wannan ma browser ce, wanda tanada dadin aiki sosai, saboda tanada sauri fiye chrome, ammade chrome itace babba fiyeda opera. Saide bakowa bane zaigane cewa chrome tafi opera ba, har sai mutun yayi aiki dasu zai gane. Itama opera tanada abunda takeyi wanda itakanta chrome batayi, misali wajen yin upload akananan hosting, zakaga opera tafi jin dadi aiki, kuma tafi chrome sauri anan, saide da chrome ana hada PDF File, yayin da a opera, ba'ayi.



Amfaninta

Dadin uploading.

Saurin downloading.

Ajiye page dan amfanin offline.

Saurin copy and paste.

Saukin yin bincike.



3. YouTube

Mafi yawan masu amfanida yanar gizo dakafafen sada zumunta, sun san YouTube, kuma sun san aikinshi, da amfaninshi dakuma gudunmurwa dayake bayarwa ga internet. To da wannan application din zaka iyayin komai na YouTube kamarsu daura bidiyo kokuma bude account nasu tareda Gmail naka.



Amfaninshi

Kallo a YouTube.

Uploading na video.

Bude account na YouTube.

Saurin nemo bidiyo.

Saving na searching.



4. KeepVid

Sarki downloading kenan! Shikuma wannan application din kamfanin KeepVid ne suka hadashi, sannan suka samasa suna dede da sunan kamfanin, kokuma suka sawa kamfananisu takwara da application din. Wannan kuma amfani shi, shine yin downloading akafafen sada zamunta, duba dacewa yawanci official application, nakafafen sada zumunta, ba'a iyayin downloading na abubuwa acikinsu, musamman ma downloading na bidiyo, shiyasa wa'annan kwararrun suka hada wannan application din, wanda amfaninshi kawai downloading ne, dakuma ganin bidiyoyi.



Amfaninshi

Sukar da bidiyo a YouTube.

Sukar da bidiyo a Facebook.

Sukar da bidiyo a Instagram.

Sukar da bidiyo a Twitter.

Sukar da bidiyo a Vimeo.

Ganin bidiyo a YouTube.

Ganin bidiyo a Facebook.

Ganin bidiyo a Instagram.

Ganin bidiyo a Twitter.

Ganin bidiyo a Memory.

Saurin downloading.



5. MX Player

Kallo kenan!! Wannan application din mutane dayawa daga cikinmu harda wa'anda basa harkar yanar gizo sun san amfanin wannan application din, saboda shi kawai kallon bidiyoyi akeyi acikinshi, kuma shi baya bukatar data domin yin kallo dashi, kuma yana bude kusan muce dukkan bidiyoyi in banda yankadan.



Amfaninshi

Kallon bidiyo.

Gogewa bidiyo.

Bude manyan bidiyo.

Ganin bidiyo tareda substitle.



6. KineMaster - Pro Video Editor

Duniyar gyaran bidiyo kenan!!! Wannan application din nide banga wani application na gyaran bidiyo awayar Android kamarshiba, saide akwai wani mai irin aikinshi, shikuma sunanshi PowerDirector.apk, to wa'annan application duk aikinsu dayane. Kuma gaskiya sunada saukin gyaran bidiyo idan mutum ya iya aiki dasu, awayar sa ta Android. Amma yana cikin space akalla 200MB, saide nauyi baifi 34MB, idan kayi installing nashi kana aiki dashi zakaga, ahankali ahankali yana cika maka space din kusan 200MB din.



Amfaninshi

Gyaran bidiyo.

Saka rubutu a bidiyo.

Saka sauti a bidiyo.

Saka transition.

Hada watermark na bidiyo.

Hada intro.



7. Background Eraser

Shikuma wannan application din, amfaninshi sai masu gyaran hotone zasu gane, saboda shi ana aikidashine, domin cire background na hoto. Cirewa hoto background, yanada dadi musanman ga yan karya wanda zakaga sun dau hoto awani guri, saikaga suncire background na wannan hoton susaka wani background din.



Amfaninshi

Cire background.

Canja fadin hoto.

Canja tsayin hoto.

Hada kanana icon.



8. PixelLab - Text on pictures


Sarki aikin hoto kenan! Shi wannan ana aiki dashi wajen hada logo, dakuma icon. Sannan ana ahada banner irinnasu facebook, twitter, youtube. Sannan ana sakawa hoto background. Ana canja fadin da tsayin hoto.



Amfaninshi

Saka background.

Hada logo ko tambari.

Hada icon kanana

Saka abubuwa ahoto.

Hada intro na bidiyo.

Goge background.



9. PicsArt Photo Studio: Collage Maker & Pic Editor


Shima wannan kusan amfaninshi dayane dana samanshi, domin dukkansu aikin dasukeyi shine gyaran hoto.



Amfaninshi

Saka background.

Yin zane wato drawing.

Hada icon kanana

Saka abubuwa ahoto.

Hada intro na bidiyo.

Goge background.



10. Es File Explore.apk

Wannan application din yana aikine bangarori dadama, sannan kuma file manager ne, ana iya boye file dashi, sannan kuma abayyanasu daga baya wanda yakunshi application dayawa. Masu gina website zasuso suyi aiki dashi musamman wajen editing na code dakuma yanda, kokuma bude theme da template.



Amfanonin Shi

File manager.

Root browser.

Rubuta code.

Kallon bidiyo.

Sauraron sauti.

Ganin hotuna.

Downloader.

Bude zip file.

Hada zip file.

Canja Font style.



Bawai muna nufin wa'annan application din, sunfi kowane application mahimmanci ba, muna nufin suma sunada nasu amfanin. Sannan kuma kuna iya temaka mana, ta duk inda kukaga munyi kuskure, kokuma munsa wani abunda kuke ganin, badede bane ace munsa a wannan shafin. Kokuma munyi wani darasin dakuke gani badede bane, kuna iyayi mana gyara, kuma kuna iya turomana naku labarin, domin mukaru dukkanmu, wasuma sukaru daku, damu baki daya.



Sannan kar agaji damu, acigaba da kasancewa da wannan shafin, kuma kar amanta, ana iya ajiye mana comment, a wajen comment da aka kebe akarkashin kowane darasi, da akaranta a wannan shafin. Sannan muna bukatar kutemaka kutura wannan darasin ga 'yan uwa, da abokan arziki, kota dandalin sada zumunta na Whatsapp, Twitter, Facebook, Instagram dasauransu. Mungode, sai mun hadu a darasi nagaba, kuhuta lafiya, sai anjima.

No comments:
Write Comments