auri mata biyu a rana daya, ya ce ya yi
hakan ne don ya karfafa wa maza
gwiwa kamar yadda ya shaida wa BBC. Saurari mai suna Bashir Mohammed ya
ce ya fara soyayya da 'yan matan biyu
ne kimanin watanni takwas da suka
wuce kafin su amince da bukatarsa ta
aurensu. "Na rika kawo 'yan matan gidana domin
su saba da ni. Kuma a duk lokacin da
muke tare da su ina fada musu yadda
nake kaunarsu. Kuma dukanninsu sun
gamsu da hakan," in ji sabon angon. "Dabarar auren mata biyu tashi guda shi
ne ba za su rika nuna tsananin kishi ba
daga bisani, saboda kowace za ta
fahimci cewa ba ita kadai ba ce," a
cewarsa. Matashin ya ce ya auri mata biyu ne
tashi guda saboda yana "son yara da
yawa". Gabilin al'ummar kasar Somaliya
Musulmi ne wadanda addininsu ya
amince musu su auri mace fiye da daya. Sai dai ba a saba ganin saurayi ya auri
mata biyu ba a rana guda, in ji wakilin
BBC Mohamed Mohamed. Ba wannan ne karon farko da hakan ya
faru a kasar ba domin ya taba faruwa a
shekarun baya, abin da ya sa wadansu
suke ganin watakila a ci gaba da raya
al'adar a kasar. Ango Bashir ya aure matan biyu ne masu
suna Iqra da Nima a ranar Juma'a a
kauyen Sinai wanda ke karkashin
yankin da ya balle daga Somaliya wato
Somaliland.
No comments:
Write Comments