Need To Contact Me :- +2349021664821

Friday, October 19, 2018

Home Shiga ku karanta Yadda za'a magance Tabon fuska ko kuraje cikin sauki

Subscribe Our Channel


tw

Assalamu Alaikum
Matsalar kuraje da tabon fuska sun shafi
bangaren matasa, mata da maza. Wani
lokaci sai an sha
wahalar.magance.kurajen fuska, amma
sai tabo ya ki bacewa. Rashin bacewar
tabo a fuska na bata. kwalliya. Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron
mutane domin wadannan tabon. Da
yawan mutane sun gwada.Magunguna, Kala Kala domin rabuwa da tabon fuska.
Wasu sun yi sa’a wasu kuma ba su yi sa’a
ba. wannan Shafi Mai Albarka yau mun zo da
bayanin yadda za a magance tabon
fuska. Muna son a.san cewa daya za.a
Zaba daga cikin hanyoyin da muka
lissafo, kada a hada su gaba daya. Domin
yin hakan zai kara lahanta fuska ne.

1- A samu ganyen dogonyaro, sai a hada
shi da kurkum, sannan sai a shafa a
fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a
wanke da ruwan dumi.

2- Za a iya shafa markadadden dankalin
Turawa a kan tabo. Hakan na magance
kurajen fuska, sannan yana.hana su sake
fitowa.

3- A daka tafarnuwa sai a shafa a kan
tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana
gyara fuska, sannan ta magance tabon
fuska.

4- a hada karas da tafarnuwa da zuma
sai a shafa a fuska na tsawon minti 20
kafin a wanke.

5- A samu hodar ‘baking soda’, sai a
hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska
zuwa minti 2 ko 3, daga nan a wanke
fuska da ruwan dumi.

tw

Da Yardar Allah Za'a Dace 

No comments:
Write Comments