Need To Contact Me :- +2349021664821

Wednesday, February 21, 2018

Home Abubuwanda Yakamata kusani Game da Hadiza Gabon. Jarumar Kannywood..

Subscribe Our Channel


tw
image ©

An haifi jaruma Hadiza Aliyu, wacce
aka fi sani da Hadiza Gabon a ranar
daya ga watan Yunin shekarar 1989
(shekaru 28 cif yau) a garin Libreville
na kasar Gabon. Daga tsatson mahaifi,
Hadiza Gabon ‘yar asalin kasar Gabon ce, amma daga bangaren mahaifiya,
Hadiza da a gida (gabon) ake kira da
Adizatou fulanin Adamawa ce da ke
arewa masa gabashin Nijeriya
tw
Hadiza Gabon ta yi karatun firamare (Primary)
da sakandirenta (Secondary) a mahaifarta
(Libreville) inda bayan ta kammala da
kyakkyawan sakamako ta ci gaba da
karatu a jami’ a don cika burinta na
zama kwararriyar lauya. Sai dai kafin ta kai ga cimma burinta na zama
lauya, sai karatun nata ya gamu da
tasgaru, inda a dole ta ajiye karatu..
'
Hadiza Gabon ta sake komawa
makaranta inda ta yi karatun difloma (Development)
akan nazarin harshen Faransanci.
Bayan ta kammala karatun nata ne ta
fara aiki a matsayin malamar harshen
Faransanci a wata makaranta mai zaman kanta Bayan koyarwa na wani dan lokaci,
Hadiza Gabon ta bar gida ta dawo
Nijeriya, inda ta fara sauka a garin
mahaifiyarta wato Adamawa, daga
bisani kuma ta koma Kaduna da nufin
shiga harkar fina-finan Hausa...
A can Kadunan ne ma Hadiza ta gamu
da Ali Nuhu
tw
wanda shi ne ya taimaka
mata wajen shiga harkar fim ka’in da
na’in. Hadiza ta fara fitowa a fim din
Artabu a shekarar 2009 Jerin Wasu Finafinai da Hadiza Gabon
ta taka rawa a cikinsu....
● Artabu (2009),
● Daina Kuka,
● Farar Saka,
● Fataken Dare,
● Jinin Mijina,
● Kolo,
● Mukaddari,
● Sakayya,
● Umarnin Uwa,
● Ziyadat,
● Wasila (2010),
● Umarnin Uwa(2010),
● Aisha Humaira (2012),
● Yar Maye (2012),
● Badi Ba Rai(2012),
● Akarizziman (2012),
● Dare Daya(2012),
● Wata Tafi wata(2012),
● Da Kai Zan Gana (2013),
● Haske (2013),
● Ban Sani Ba(2013),
● Mai Dalilin Aure (2014),
● Daga Ni Sai Ke (2014),
● Ali Yaga Ali (2014),
● Basaja(2014),
● Daga Ni Sai Ke (2014),
● Uba Da ‘Da (2015),
● Indon Kauye(2015),
● Ba’asi (2015),
● Jarumta(2016).....,,

Nasarorin Da Hadiza Gabon ta samu Tun bayan sanya kafarta a harkar film din Hausa,
Hadiza ta samu nasarori da
dama da suka hada da:
Gwarzuwar
jarumar shekara a shekarar 2013 na
Best Of Nollywood Awards a fim din
Babban Zaure. A wannan shekarar dai, Hadiza Gabon ta samu wani kanbi
daga gwamnatin jahar Kano da aka yi
wa lakabi Kwankwasiyya Award bisa
kokarinta wajen habaka harkar fim

a jihar A shekarar 2014 ma
Hadizar ce ta
lashe kanbin gwarzuwar shekara na
Kannywood MTN Awards karo na biyu
a fim din Daga Ni Sai Ke A shekarar 2015 Gabon ta sake lashe
kanbin mataimakiyar babbar jaruma
a bikin karrama ‘yan wasa
na Kannywood AWA 24 Film & Merit
Award a fim din Ali Ya Ga Ali Ko a bara ma dai sai da Gabon ta sake
lashe wani kanbin na gwarzuwar
shekara a bikin karrama ‘yan wasa
na African Hollywood Awards Haka kuma, Hukumar Kula Da
Makarantun Sakandire ta Jihar Kano
sun mika takardar Yabo ga Hadiza
Gabon bisa tallafawa harkar ilimi da
jarumar ke yi a makaratun jihar Sai kuma kungiyar Statup Kano da ta
mika irin waccan takardar Godiya da
Yabawa ga Hadiza Gabon bisa
tallafawa masu kananan sana’o’i a
jihar Kano Shekarar 2016, Hadiza Gabon ta kafa
wata gidauniyar taimakawa masu
karamin karfi da nakasassu da ta yi
wa lakabi da HAG Foundation
(Gidauniyar Hadiza Aliyu Gabon).
Gidauniyar an kafata ne da nufin tallafawa masu ‘yan gudun hijira a
harkar ilimi da lafiya. Wannan ya
sanya ta zama mutum ta farko a
Kannywood da kafa gidauniya da irin
wannan manufar Ko a watan Maris na shekarar 2016 Hadiza Gabon ta kai
wata ziyarar tallafi sansanin gudun
hijira da ke jihar Kano,
tw

inda ta bada
tallafin kayan abinci da suturu da
wasu kayan bukata ga ‘yan gudun hijiran Hadiza Gabon, jakadiya ce ga
kamfanonin MTN Nijeriya da taliyar
Indomie
'
muna mata fatan Allah ya ja
mata gora. Allah ya sa ta dade tana yi, amin
pls Share To Facebook

No comments:
Write Comments