Umar Muhammad Sharif
fitaccen mawakin fina-finan
Hausa ne,
a hirar da ya yi da
Aminiya a ranar Lahadin da ta
gabata ya bayyana yadda ya
fara waka da irin nasarorin da ya samu da kuma wasu daga
cikin kalubalen da ya fuskanta.
Tarihin Umar M Shariff
A Takaice
Assalamu alaikum,
Kamar Yanda kowa yasani
sunana
Umar Muhammad Sharif, A an
haife ni a Rigasa da ke Jihar
Kaduna a shekarar 1987. Nayi
makarantar Primary da
secondray duk a Rigasa. Dalilin da ya sa na zabi sana’ar
waka,
Waka ta fado mini ne lokaci guda kwatsam da
rana tsaka ne, amma a gaskiya
ban taba tunanin zan yi sana’ar
waka ba, saboda tun tasowata ni dalibi ne, ina karatun boko
da na addini, na ma fi bada
karfi a bangaren addini,
Silana na fara waka kuwa ita ce akwai
wata budurwa da nake
matukar so da kauna, amma na kasa sanar da ita abin da ke
zuciyata. A gaskiya jin nauyin abin shi ne
ya hana ni sanar da ita. Nakan
je har kofar gidansu, na aika a
yi mini sallama da ita, amma
inda gizo ke sakar shi ne da
zarar ta fito don ganin wanda ke neman ta, sai na buya, ta
gama dube-dube nta daga nan
idan ba ta ga kowa ba sai ta
koma gida. To na yi hakan
kusan har sau uku ba tare da
samun damar tsayawa da ita ba. Daga nan wata rana sai na
yi ta maza na ce zan ga abin da
zai ture wa buzu nadi. Da na je sai na aika kamar
yadda na saba amma sai a
wannan karon ba ta fito ba. Na
yi ta jira amma shiru kake ji. To daga nan ne fa kamar wasa
sai na fara yin waka a kan halin
da na samu kaina ciki. Daga
kofar gidansu na fara waka har
na isa gida ban daina ba. Haka
nayi tayi duk lokacin na tuna da wannan baiwar Allah. A cikin wannan halin ne sai na
samu biro da takarda na rubuta
wakar. Akwai wani mawaki
Ibrahim Suleiman (Zaki) wanda
ya kasance abokin yayana ne. Kamar wasa da ya ga wakar
kuma ya umarce na rera ta.
Bayan ya saurari wakar sai ya
ya ba kuma ya yi min wasu
gyararraki, kana ya karantar da
ni kabli da ba’adin waka. Daga nan ne fa na fara waka gadan-
gadan.
daga gida, daga bisani muka
fahimtar da iyayen mu. Bayan
ba su ga canji daga irin
tarbiyyar da suka yi mana ba,
sai suka fara sa mana albarka da fatan alheri. Shakka babu
addu’o’insu na tasirin sosai a
kan nasarorin da muke ci gaba
da samu.
a kalla wakokina za su kai 600
Kundin waka Duka wakokina. Fitowa a fim Ina fitowa a fim,
sannan nakan shirya nawa.
Fina-finan da na fito sun hada
da:
‘Mahaifiyata’ da
‘Nas’
Mansoor".
Fina-finan da na
shirya sun hada da:
‘Ba Zan Barki Ba’
’Ka So A So ka’ da
Biography of Umar M. Sharif BURINA Ba ni da wani burina saboda ko
yanzu kasuwa ta watse dan
koli ya ci riba.
.Sunana ya kai
duk inda ba ka zato, saboda na
sha samun kira ta waya daga
Amurka da sauran kasashen duniya, wanda jama’a ne masu
sauraren wakokinmu ke yaba
mana.
IYALAI Ina da mata daya Maryam da
Yarana ga nan Hoton Yaran Jarumi Umar M Sharriff
.mun gode Contact Admin +2349021664821
No comments:
Write Comments