Need To Contact Me :- +2349021664821

Sunday, April 7, 2019

Home BUHARI:- Yan Najeria Basuyi Min Adalci Ba Akan Kisan Zamfara - Inji Buhari

Subscribe Our Channel


Shugaba Muhammadu Buhari ya bara kan kashe-kashen da ake fama da shi a jihar Zamfara, inda ya mayar da martani ga masu zangar-zangar Allah-wadai da al'amarin. Buhari ya ce kare dukiyoyi da rayukan 'yan Najeriya su ne abin da ya saka a gaba a kodayaushe, saboda haka rashin adalci ne a ce bai damu da abin da yake faruwa ba. Yana wannan batu ne daga yankin Gabas Ta Tsakiya, inda yake amsa gayyatar wasu sarakunan Larabawa don shiga taron tattalin arziki na duniya.    "Shashanci ne da rashin adalci a ce ban damu da abin da yake faruwa ba a Jihar Zamfara ko kuma a ce ba na yin komai game da lamarin," Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter. Ya kara da cewa "kare dukiyoyi da rayukan 'yan Najeriya su ne abin da na saka a gaba a kodayaushe. Babu wani abu da ya sha gaban haka." Ya ci gaba da cewa: "A shirye muke don kawo karshen wadannan tambadaddun 'yan bindiga. Mun tura jami'an tsaro zuwa lungu da sako inda abin ke faruwa kuma muna kara azama. "A kodayaushe ina samun bayanai daga jami'an tsaro a kan abin da ke faruwa a kasa baki daya. Ina tabbatar maku cewa za mu ci gaba da yin iyakar kokarinmu don karfafa wa jam'ian tsaro gwiwa su tunkari lamarin da karfin da ya dace". A cewar shugaban "Ina so in jawo hankalin 'yan Najeriya da kada su siyasantar da wannan al'amari na Zamfara. Ta yaya zan kawar da kai daga wannan kashe-kashen rashin imani na 'yan kasata da kuma halin ni-'ya-su da suka samu kansu a ciki? "Bari in kuma mika sakon ta'aziyyarmu ga wadanda abin ya shafa da kuma 'yan uwansu da masoyansu. Muna jin abin da kuke ji kuma babu abin da ya fi muhimmanci a wurina sama da in ga an kawo karshen wadannan 'yan fashi", in ji Shugaba Muhammadu Buhari. A karshen makon nan ne 'yan Najeriya na ciki da wajen kasar suka yi zanga-zangar nuna Allah-wadai da halin da jihar Zamfara ke ciki. Sun zargi Shugaba Buhari da nuna halin-ko-in-kula da kuma yin kira da ya dauki matakin gaggawa, ciki har da ayyana dokar ta-baci a jihar.     

No comments:
Write Comments