Need To Contact Me :- +2349021664821

Friday, April 5, 2019

Home SIYASA:- Yanda Salon Abba Gida Gida Ya Yarikita Siyasar Jihar Kano

Subscribe Our Channel


CP Wakili, Abba Kabir, Ganduje



Image captionBa a iya bayyana wanda ya lashe zaben na Kano ba har sai da aka shiga zagaye na biyu
Masu iya magana na cewa siyasar Kano sai Kano,
 kuma a ko da yaushe ta kan zo da wani abu sabo, kamar yadda a bana salon Abba gida-gida da makamantansa suka hadu a yunkurin 'yan hamayya na kifar da jam'iyyar APC mai mulki.
Masu sharhi da dama sun yi hasashen Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai samu wa'adi na biyu cikin sauki ganin yadda rikici ya dabaibaye jam'iyyar adawa ta PDP da kuma tsagin Kwankwasiyya wadanda su ne manyan masu adawa da gwamnan karkashin jagorancin mutumin da ya gada Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.


Amma sai ga wankin hula ya kai APC da Ganduje dare, inda aka tafi zagaye na biyu, kuma PDP ta kasance a gaba da ratar kuri'a 26,655. Kafin daga bisani INEC ta bayyana APC a matsayin waccee ta lashe zagaye na biyun da tazarar kuri'a 8,982 jumulla.

No comments:
Write Comments