Yanda Ake Bude Sabon Email Na Yahoo
Abaya munyi bayani, akan yanda ake bude Gmail, kuma mun nuna yanda ake verification nashi, harma muntura masa sako, amma gamasu aiki da symbian. Kodayake harma masu aiki da Android dinma, munyi musu bayanin yanda ake bude Gmail, to shine muka yanke shawarar nuna muku yanda ake bude Yahoo Mail cikin sauki.
Gaskiya, bude Yahoo Mail bashida wata wahala, amma ga masu aiki da wayar Android, domin cikin minti hudu zaka iya gama komai da komai, harda verification nashi. Saide ina baka shawara wajen password, kayi amfani da password maikarfi(strong password), sannan kuma kasaka recovery email da recovery phone number.
Shima Yahoo Mail yanada nashi amfanin, kamar yanda mukayi bayanin amfanin Gmail, saide shi Yahoo Mail baikai gmail tsaroba, amma shima yanada tsaro sosai, tunda daga Gmail saishi afannin tsaro, acikin kamfanin email dana sani a duniya.
Inaga Yahoo Mail, kusan shine email na biyu damutane sukafi aiki dashi bayan email na kamfanin Google wato Gmail. Shima ana amfani dashi wajen saka website a searching engine, amma saide a Bing ko Yahoo akesawa, yayinda shikuma gmail kawai a Google ake aiki dashi.
Abubuwan Da'ake Bukata
Kakaranta wannan tutorial din gaba daya.
Kasaukar da application na Yahoo.
Ga Yanda Akeyi
Dafarko, kayi downloading na wannan application din, sakayi installing nashi. Idan kagama installing nashi, sai kabude wannan application din, zakaga yanuna maka YAHOO! MAIL atsakiya, sai kayi kasa kashiga inda aka rubuta Create a Yahoo account.
Daga nan zaikaika gurin Sign up, wato wajen bude sabon account kenan. Saikasa sunanka, agurin rubutu na farko, misali Nura. Gurin rubutu na biyu kuma kasa sunan mahaifinka, kokuma wani suna daban, misali Mahdi. Sannan kasa sunan dakakeso yazama shine adreshin email dinnaka, misali kasa nura.mahdi, kenan zaizama nura.mahdi@yahoo.com. Saikuma gurin saka password, shima kasa password naka, amma yanadakyau kasa password mai karfi. Daga nan kuma saikasa lambar wayarka, agurin saka lambar waya kusada ita zakaga, Country code, wanda +234, amma ga mutanen Nigeria. Daga nan kuma sai kazabi watan da'aka haifeka, misali May. Gaba dashi kadan kasa nawa gawata aka aifeka, misali 05, sannan kazabi awace shekara aka aifaka misali 1995. Kana gama cike wa'annan gurin, sai kazabi jinsinka wato namiji ko mace Male namiji, dakuma Female mace. Sannan kayi kasa kadanna Continue.
Daga nan zatakaika gurin da zakayi verifying na account naka. Daga can sama zakaga lambar wayarka, saikaduba kasa kadanna inda aka rubuta Text me an Account key.
Daga nan, zasu turo maka sako ta cikin layinka, saikazo kabude wannan sakon, ka kwafo wannan lambobi dasuka turo maka, sai kadawo cikin application na Yahoo din kasasu, saika danna Verify shikenan. Kana gama Verify din, zasu nuna maka sakon congratulation, wato suna tayaka murnar bude sabon email nasu. Daga nan zatakaika cikin email naka, kuma zakaga wasu sakonni.
Bayanin Kammalawa
Yana dakyau bayan kazabi sunan adreshin email, idan sukace ma akwai mai wannan sunan to kakara wasu lambobi. Misali kazabi nura.mahdi idan akwai mai wannan sunan sai kakara wasu lambobi kamar nura.mahdi223 kuma gurin lambobin sirrin wato password, kayi amfani alamomin rubutu wato Symbols wanda ake kiransu da Special characters, saboda yanzu akwai azzaluman mutane, da suke mugunta suna kwacewa mutane email nasu. Amma idan kasa lambbobin sirri mai wahala ganewa, to zaka samu tsaro cikin ikon Allah.
Yana dakyau, bayan kagama bude sabon adreshin Yahoomail, kabude kaje kasa Recovery email. Recovery email wani email ne dazaka saka, koda wannan email din naka yasamu matsala zaka iyaseta komai, ta hanyar amfani da shi.
Sannan akwai Recovery number, nan shima duk lambar dakasa, da ita zakayi amfani wajen dawoda account naka, koda kamanta password ne.
Nan shine karshe wannan tutorial din, akan yanda ake bude yahoomail. Sannan kuma kuna iya temaka mana, ta duk inda kukaga munyi kuskure. Domin kowane mutum yakanyi kuskure, kuma kuna iya turomana naku tutorial din, domin mukaru dukkanmu, wasuma sukaru daku, damu baki daya, haka shine agudu tare atsira tare.
Sannan karkuma manta, kuna iya ajiye comment naku, a wajen comment da aka kebe akarkashin kowane darasi, dakuka karanta a wannan shafin. Sannan muna bukatar kutemaka kutura wannan darasin ga 'yan uwa, da abokan arziki, kota dandalin sada zumunta na Whatsapp, Twitter, Facebook, Instagram dasauransu. Mungode, sai mun hadu a darasi nagaba, kuhuta lafiya, sai anjima.
No comments:
Write Comments