Shahararriyar jarumar nan ta wasan fina- finan Hausa a Kannywood kuma 'yar asalin jihar Kano mai suna A'isha Aliyu da ake yi wa lakani da A'isha Tsamiya ta fito ta bayyanawa duniya babban dalilin da ya sanya ita bata saka kananan kaya kamar sauran wasu jaruman fim. Jarumar dai ta bayyana cewa ita ba ta sa kananan kaya ne musamman saboda dalilin cewa ba sa yi mata kyawu idan ta saka su don kuma ta dan gwada a lokutan baya. Kamar yadda aka sani cewa wasu da daga cikin jarumai mata a masana'antar fim su kan sanya kananan kaya a yanayin rayuwar su ta yau-da-kullum ko kuma ma a cikin fim amma ba'a taba ganin ita A'isha Tsamiya da su ba. A kwanan baya ne wata kungiya a arewacin kasar nan tayi kira ga matan yankin da Suyi koyi da dabi'u da kuma Jajircewa Irin na jaruma Rahma Sadau wanda kuma hakan ya jawo cece-kuce a yankin inda ake ganin hakan bai daceba duba da yanda Jarumar take saka kananan kaya da sauransu.
Sunday, February 18, 2018
Subscribe Our Channel

Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Write Comments