Need To Contact Me :- +2349021664821

Monday, April 30, 2018

Home Abubuwan da yakamata shgaba buhari yayi wa Kannywood - inji Darakta Kamal s Alkali

Subscribe Our Channel


tw
image ©
Fitaccen daraktan fina-finan Hausa,
Kamal Sani Alkali ya ce abubuwan da
yake so Buhari ya yi wa masu shirya
fina-finan Hausa na Kannywood su ne, ya
sanya gwamnatin tarayya ta samar da
tsare-tsare na musamman da za su sanya masana’antar ta rika samun ci gaba mai
dorewa. Daraktan, wanda shi ne shugaban
Kamfanin Kamal International Limited
mai babban ofishinsa a Kano ya yi
wannan kiran ne a lokacin da yake
tattaunawa da wakilin Aminiya ta
wayar tarho. Alkali wanda ya bada umarni a manyan
fina-finai da suka hada da ‘Umar Sanda’
da ‘Sahabi’ da kuma ‘Guguwar So’ ya ce,
rashin isasshen jari a wurin ’yan fim da
karanci sinimomi da kuma matsalar satar
fasaha ne suka hana Kannywood bunkasar a-zo-a-gani, inda a yanzu
masana’antar take cikin wani hali. Ya ce, “Ina so gwamnatin Buhari ta gina
manyan sinimomi a Arewacin kasar nan,
sannan ta ba ’yan fim bashin da babu
kudin ruwa a cikinsa, ko tallafa wa ’yan
fim da jari, ko dai ta ba su bashin da babu
kudin ruwa a cikinsa don su gina sinimomin a Arewa. “Idan gwamnatin Buhari ta yi hakan, to
Kannywood za ta bunkasa, bunkasar da
za ta sa ta rika gogayya da manya-
manyan masana’antun fina-finai na
duniya,” inji Kamal.
Daraktan wanda ya lashe Gwarzon Darakta yayin Gasar City People
Entertainment ta 2017 ya kuma bukaci
gwamnatin Buhari ta samar da
ingantacciyar hanyar yaki da masu satar
fasaha ko barayin zaune da suka addabi
masana’antar fiye da shekara 15. Ya ce, “Kannywood tana cikin ta
mawuyacin hali, zan iya cewa ta kusa
durkushewa saboda masu satar fasaha
da barayin zaune. Kada a manta kafin
kowane fim ya fita sai an biya Hukamar
Kare Hakkin Mallaka ta kasa Naira dubu 15, sannan a biya Hukumar Tace Fina-
finai ta Jihar Kano Naira dubu 10 da dari
500, amma hukumomi sun kasa samar da
nagartacciyar hanyar yaki da masu satar
fasaha.” Alkali wanda ya tsara labaran fina-finai
irinsu, ‘Jarumin Maza’ da ‘Gaba Da
Gabanta’ ya kuma shawarci gwamnatin
tarayya da ta zuba jari a masana’antar
don ganin an samar da fina-finai masu
inganci.

No comments:
Write Comments