Canja background yanada dadi, musamma ga wa'anda sukeson susaka hotonsu akusa da wani gida kokuma wata mota, kokuma wani gurin shakatawa. Akwai wasu hanyoyi dadama da'ake canja background, amma awannan darasin zamuyi aiki da wasu application guda biyune, nafarkon zamu cire masa background dayan kuma nasaka background ne.
Mafi yawa munfi sanin ana canja background na hotone da computer. To kamar yanda akeyi da computer awayama anayi, domin kwanan baya nacaja background, a symbian, amma awannan darasin zamuyine aka Android. Karde nacikaku da surutu bari mufara, saide kafin nan kanemi kayan aiki, sune guda biyu saikuma hotunan ka.
Abubuwan Da'ake Bukata
Kasaukar da Background Anan.
Kasaukar da Eraser.apk.
Kasaukar da PixelLab.apk, awayarka.
Awannan darasin zamu canja background na hotone, wato zamu goge asalin background din hoton, musaka masa background dinda mukeso. Dafarko ga hoton da zamucirewa background, musaka masa wani background.
Nan kuma bayan muncanja masa background ne, kunga irin background dinda muka saka masa.
Ga Yanda Akeyi
Dafarko, kabude Eraser, saikadanna kan Load a photo, daga nan zata tambayeka Choose an action, saikadanna kan Gallery. Daga nan zata kaika cikin Gallery, saikaje inda wannan hoton dazaka canjawa background yake, saikadanna kanshi. Kana danna kanshi zaibude maka hoton, saikadanna Done, yana daga can sama abangaren dama.
Yauwa, yanzu munzo gurin goge background, idan kaga dama zaka iya goge background dinda Manual, wato kana goge yanda kakeso kenan, amma gwara kayi aiki da Auto, saboda shi idan kashiga shi zai goge maka background din, sannan saikadawo Manual kagama gogewa. Yanzu kawai saikadanna kan Auto.
Saika goge background din gabadaya. Idan kagama goge background din, sai kayi saving nashi, domin yin saving kadanna Done, zaka ganshi acan sama daga bangaren dama.
Sannan saika kara danna Save, shima yanacan daga bangaren dama ta sama, yanzu mungoge wa wannan hoton background nashi, kawai saura muyi saving nashi, sannan muje musaka masa background dinda mukeso.
Shikenan angama komai saika danna Finish. Yanzu angama da matakin farko wato mungoge background nahoton, sannan kuma munyi saving nashi, saura musaka masa background narammu.
Bari kuma mufara da mataki na biyu wato sakawa wancan hoton background, amma zamuyi aiki da background dinda yake zuwa acikin wannan application din wato PixelLab.apk. Yanzu kuma sai kaje kabude PixelLab.apk, zakaga wani rubutu atsakiya, kamar haka New Text, kawai kagogeshi, idan zakagoge shi kaduba daga sama zakaga alamun kwandon shara daga can sama kadannashi zai tambayeka kamar haka Delete the selected object?, saika danna Ok.
Yanzu, mungoge wannan rubutun, saura kuma mudakko wancan hotonda muka goge masa background dafarko. Yauwa kaduba can sama daga bangaren hagu, zakaga wani icon kamar plus(+), kadannashi zainuna mawasu rubutu kusan shida, kaduba cikinsu saikadanna kan From gallery, daga nan zai nuni ma Choose an action, kawai kadanna kan gallery, idan yabude maka gallery kaduba zakaga wata folder maisuna Eraser saikabude ta, acikinta zaka samu wancan hotonda kagogewa background.
Kana danna wannan hoton, zakaga yabude maka wajen resizing na hoton, wato wajen ragewa hoton tsawo da fadi, kawai kadanna kan wannan arrow guda hutu dasuke tsakiya akasan hoton. Saikuma kasake danna kan wancan alamar, mai kamada marking din nakarshe, daga bangaren dama.
Yauwa tunda yanzu mun dakko hoton dazamu sawa background. Kaduba daga kasa kadanna wancan alamar mai kamada littafi, wanda dagashi saina karshe abangaren dama. Kana danna kan wancan alamar saika duba, zakaga Image, Sai kashiga Image din, zakaga tanuno maka hotunan da ake sawa a background daga can kasa, hotun nan farko, zakagansu kamar paper, to saika jawosu, daga daga zuwa hagu(swipe from right to left) domin kazabi, wanda kakeso, sannan kadanna kanshi. Bayan kazabi background saika matsarda hotonka inda kakeson yazauna, kamar yanda kake gani nasaka, nawa abangaren dama. Kaima saika matsar dashi inda kakeso.
Hamma!!! Yanzu aiki yazo karshe, tunda mungama saka background, abuda yarage shine muyi saving na hoton. Domin yin saving nahoton, kaduba daga can sama, zakaga wani icon maikada memory card, to kawai ka dannashi, zai nuno maka zabi guda biyu, kawai saikadanna nabiyun wato Save as image, zai nuna maka wajen yin share kawai saika danna Save to gallery, zai danyi wani loading kadan sannan yayi saving shikenan.
Aiki!!! Yanzu de an kammala komai. Kuma ga hoton nan.
Amma fa yanada kyau kaseta hotonka tayanda kakeso, kuma zaka iya matsar da hoton ka kakaishi duk inda kakeso.
Nan shine karshe wannan darasin, kuma kuna iya temaka mana, duk inda kukaga munyi kuskure, kokuma munyi wani abunda kuke ganin, baidace ace munsa a wannan shafinba, kuma kuna iya turomana naku labarin, domin mukaru dukkanmu, wasuma sukaru daku, damu baki daya.
Sannan karkuma manta, kuna iya ajiye comment naku, a wajen comment da aka kebe akarkashin kowane darasi, dakuka karanta a wannan shafin. Sannan muna bukatar kutemaka kutura wannan darasin ga 'yan uwa, da abokan arziki, kota dandalin sada zumunta na Whatsapp, Twitter, Facebook, Instagram dasauransu. Mungode, sai mun hadu a darasi nagaba, kuhuta lafiya, sai anjima.
Awannan shafin akoyada yaushe mukanyi farin ciki daku, sannan mukanyi bayani isasshe da hausa domin shine yaren damukafi amfani dashi a wannan yankin namu.
No comments:
Write Comments