Instagram yana daya daga cikin shafukan sada zumunta wanda matasa suke amfani dashi kullum domin susada zumunci a tsakanisu, kuma ana iya tura sakon hoto dakuma bidiyo acikinshi, shima a Instagram duk bidiyoyin da'ake daurawa babu damar ayi downloading nasu, saide akwai wata hanya da ake downloading nasu, wanda mutane dayawa basusan yanda akeyiba.
Shikuma Instagram duk bidiyon, da'ake daurawa, tsayinsu baya wuce minti daya(1 minute), mafi yawanci ma anfisaka bidiyoyin nishadi da ban dariya(comedy). Kuma wasu daga cikin masu amfani da shafin Instagram sukanso suyi downloading na wa'annan bidiyoyin, musammanma biyoyin comedy, amma sunkasa downloading nasu, to idan kakaranta wannan darasin, zaka koyi yanda ake downloading na bidiyo a Instagram, cikin sauki alokaci kalilan.
KeepVid wani kamfanin kera application ne, kuma sunkera wani application mai sunan kamfanin wato KeepVid.apk, wanda akwai nau'in na computer, sannan kuma akwai nawaya, shi amfanin wannan application din shine yin downloading na bidiyo akan shafukan sada zumunta. Ganin cewa mutane dayawa basusan yanda akeyiba.
Baride mufara karmucikaku da surutu, amma yazamanto kanada account din Instagram, wanda yake aiki.
Abubuwan Da'ake Bukata
Kasaukar da KeepVid application.
Karanta wannan darasin gaba daya.
Ga Yanda Akeyi
Dafarko kayi downloading na wannan application din, maisuna KeepVid.apk, sannan kayi installing nashi. Idan kagama installing nashi, saika budeshi, daga can sama zaka logos wato tambarorin shafukan sadarwa dayawa, kaduba acikinsu zakaga tambarin Instagram, agaban tambarin YouTube, da Facebook, daga bangaren hagu. Saika danna kanshi(tambarin Instagram din).
Daga nan zaikaika cikin shafin Instagram din. Kawai saika danna kan Log in.
Yanzu kuma sai saka bayananka na shiga Instagram, wato username, ko email, ko lambar waya, dakuma password, naka nashiga cikin shafin Instagram. Sannan saika danna wancan madannin na Log in.
Kana shiga cikin Instagram din, zasu nemi wai kayi installing na application nasu, kawai kasharesu, tahanyar danna inda aka rubuta Not Now.
Bari zannuna muku yanda ake downloading na bidiyo a shafin Instagram, ta hanyar yin downloading na wani bidiyo da bbchausa, suka daura ashafinsu na Instagram, wanda akafi sanida @hausa, inda sukayi hira da tsohon shugaban kasar Tarayyar Nigeria, maisuna Chief Olusegun Obasanjo. To domin yin downloading na bidiyon, saikayi searching na inda bidiyon yake. Kawai kadanna kan wancan abunyin searching din, dayake can kasa.
Kasa sunan wanda yadaura bidiyon dakakeson kasauke, ni abangarena nayi searching din sunan bbchausa. Sannan saika danna sunan wanda yadaura bidiyon, acikin sakamakon bincikenka, nide nadanna sunan bbchausa.
Daga nan saika danyi kasa dakan, zakaga bidiyoyi da hotunan da wancan yadaura ashafinsa na Instagram, nide nadanna kan bidiyon, dazanyi downloading nashi, kaima saikayi yanda nayi.
Bidiyon zaibude sannan yafara playing(nunawa), kawai kayi pause nashi, wato dakatar dashi, saika danna wancan madannin dayake jikin bidiyon wato Download, dansaukar da bidiyon.
Daga nan zai fara analyze, sannan yanuna maka Save as: kawai kadanna kan Mp4.
Kana danna kan wancan Mp4 din, zata nuna maka Task added successfully, ma'ana bidiyon yafara downloading kenan.
Nan yanda bidiyon yake downloading ne, saika dan jira kadan yagama zuwa gaba daya.
Hamma!!!
Shikenan! Yanzu mungama komai, kawaide abunda yarage shine, muje kan memory card, muga bidiyon. Idan kanaso zaka iya sake downloading na wani bidiyon a youtube ta wannan hanyar damuka nuna muku acikin sauki, da wannan application.
Bayanin Karshe
Da wannan application din zaka iya downloading na bidiyo a YouTube, da Facebook, da Twitter, da Instagram, dasauransu. Amma bayanin yanda zakayi kasaukar dasu bidiyoyin a wa'annan shafukan yana nan tafe kawai kukasance da wannan shafi. Amma kusani akwai wani irin wannan application din a Playstore, maisuna KeepVid Lite, shima kuna iyayi dashi ammade kusani baikai na asalin kamfanin KeepVid kyau dakuma yin abubuwa dadamaba, inagashi acikinshi ba'a iya donwloading a YouTube, dasauran shafukan.
Nan shine karshe wannan darasin, kuma kuna iya temaka mana, ta duk inda kukaga munyi kuskure, kokuma munsa wani abunda kuke ganin, baidace ace munsa a wannan shafinba, kokuma munyi wani darasi dakuke gani badede bane, kuna iyayi mana gyara,kuma kuna iya turomana naku labarin, domin mukaru dukkanmu, wasuma sukaru daku, damu baki daya.
Sannan karkuma manta, kuna iya ajiye comment naku, a wajen comment da aka kebe akarkashin kowane darasi, dakuka karanta a wannan shafin. Sannan muna bukatar kutemaka kutura wannan darasin ga 'yan uwa, da abokan arziki, kota dandalin sada zumunta na Whatsapp, Twitter, Facebook, Instagram dasauransu. Mungode, sai mun hadu a darasi nagaba, kuhuta lafiya, sai anjima.
No comments:
Write Comments