assalamu alaekum maxiyarta yau munkawo muku yanda xaku
Ciro sautin waka, kokuma ciro muryar bidiyo, yazama sautin muryar, yanada amfani, musamman ga wa'anda suke son jin waka, kokuma masu sauron wannan abun.
Ciro sautin murya, bawai sai waka kadai ake cirowaba, har karatuma kana iya cirowa. Misali idan kana kallon bidiyoyin larabawa awayarka, idan akwai inda yaburgeka kuma kakeson kaciroshi ajikin bidiyon, kawai kamaidashi murya, domin kana sauraron lokacin dakaga dama. kasani duk wata murya ko sauti ajikin bidiyo ana iyacirosu ajikin bidiyo, ta wannan hanyar dazamu nuna muku.
Masu daura bidiyoyi a youtube, wannan haryar dazamu nuna muku tanada amfani sosai agaresu, domin suma suna saka background music, wato wani dan kida, ko waka dazakaji lokacin dakake kallon bidiyo a youtube, dakuma sauran bidiyoyi.
Abubuwan Da Ake Bukata
Bidiyon dazaka ciro muryassa.
Application maisuna Video Cutter.
Kakaranta wannan darasin gaba-daya.
Ga Yanda Ake Ciro Sautin
Dafarko kasakko da wannan application, maisuna Video Cutter. Bayan kasakko dashi sai kayi installing nashi awayarka, saikabudeshi bayan kagama installing. Idan yabude saika danna inda aka rubuta Extract MP3.
Daganan zata nuno maka bidiyoyin wayarka gaba-daya, hadda wanda suke kan waya dakuma wa'anda suke kan memory, daga nan saikazabi bidiyon dakakeson kaciro muryassa, saikadanna akanshi.
Bayan kazabi bidiyon dazaka ciro sautin nashi, zatanuno maka gurin dazaka saka sunan sautin dazaka ciro. Amma idan kaga dama basaika saka sunanba, kawai kana iyabarinshi dasunan wancan bidiyon tahanyar danna OK kawai, kokuma kawai kasa masa sunan dakakeso saikadanna OK.
Daganan zatafara ciro sautin daga cikin bidiyon daka zaba, kawai saikadan jira acikin minti daya, kokuma minti biyu, kodai wani abu makamancin haka.
Bayan tagama ciro sautin daga jikin wancan bidiyon, zaka iya turawa wani nantake tahanyar danna Share, kuma zaka iya gogeshi tahanyar danna Delete, kuma zaka iya suraron sautin, domin sauraronshi kawai kadanna inda aka rubuta Play.
Daganan zatafara playing na muryar, kawai saika saurari abunka, yadda ranka yakeso.
Domin samun wannan sautin daka ciro ajikin bidiyon kawai kaje kan memory kokuma kan waya zakaga wata folder maisuna Vcutter, acikinta zakaga wata folder maisuna ExtAudio, acikin wannan folder zaka samu wannan sautin dakaciro.
Bayanin Kammalawa:
Yanzu de mun nuna muku yanda ake ciro sauti acikin bidiyo. Daga baya kuma har mun saurari sautin damuka ciro. Sautin da ake cirowa ta wannan haryar da muka nuna, yana zuwane maikyau, kuma a .mp3 yake zuwa. Awannan hanyar ba'a bukatar Rooting, kawai wannan application din shikadai yabiya bukata.
Nan shine karshe wannan darasin, kuma kuna iya temaka mana, ta duk inda kukaga munyi kuskure, kokuma munyi wani abunda kuke ganin, baidace ace munsa a wannan shafinba, kuma kuna iya turomana naku labarin, domin mukaru dukkanmu, wasuma sukaru daku, damu baki daya, haka shine agudu tare atsira tare.
Sannan karkuma manta, kuna iya ajiye comment naku, a wajen comment da aka kebe akarkashin kowane darasi, dakuka karanta a wannan shafin. Sannan muna bukatar kutemaka kutura wannan darasin ga 'yan uwa, da abokan arziki, kota dandalin sada zumunta na Whatsapp, Twitter, Facebook, Instagram dasauransu. Mungode, sai mun hadu a darasi nagaba, kuhuta lafiya, sai anjima.
No comments:
Write Comments