Wani Bawan Allah mai suna Chukwuka
Jerri ya bada labarin yadda wasu
Musulmai su ka sha da kyar a a hanya
lokacin da rikicin Filato ya barke a
karshen makon nan. Rikicin dai tsakanin
Fulani da ‘Yan kabilar Birom yayi sanadiyyar mutuwar mutane da-dama. Mista Jerri ta shafin sa na Tuwita mai
suna MaziMum yace wani Abokin aikin
sa da ya je rubuta wata jarrabawa a
Garin Jos ya gamu da ha’ula’i a hanya
inda wasu mutane su ka tare su a hanya
su na binciken ko Musulmai ne su ko kuma Kiristoci. Wannan mutumi yace Abokin na sa ya
taki sa’a bayan da aka gano cewa duk
Kiristoci ne a cikin Motar in ban da wata
Mata guda kacal. Don dole dai wannan
mata ta cire Hijabin ta gudun kar ayi
mata yankan rago kamar yadda ake yi wa sauran Musulmai. Bawan Allan yace a gaban sa aka rika
fasa kan wasu Musulmai da ke dauke da
kayan miya kamar kwallon kwa-kwa.
Wasu matan dai sun sha ne don kurum
an gan su dauke da jariri a baya amma
da ta su ta kare kamar yadda wannan mutumi ya fada. An dai kashe mutane fiye da 100 a Garin
Barkin Ladi kamar yadda wannan
Bawan Allah ya bayyana. Kun ji labari
cewa dole dai jiya Gwamnatin Jihar ta
sa dokar ta-baci domin kar rikicin
tsakanin Fulani da ‘Yan kabilar Birom ya fi karfin hukuma. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya
koka da ta’adin da aka yi a Garin na
Filato inda yace kisan da aka yi bai yi
masa dadi ba kuma abin Allah-wadai ne.
Tuni ma dai Mataimakin Shugaban Kasa
Yemi Osinbajo ya hau jirgi ya leka Yankin da abin ya faru.
No comments:
Write Comments