Need To Contact Me :- +2349021664821

Saturday, December 29, 2018

Home Duk Talakan Da Bai Zabi Buhari Ba Bai San Ciwon Kansa - Cewar Wasu Manazarta

Subscribe Our Channel


tw
Duk Talakan Da Bai Zabi Buhari Ba Bai San
Ciwon Kansa - Manazarta
Wasu matasa masu bibiya gami da
binciken ayyukan Shugaban Kasa
Muhammadu Buhari a jihar Kano, Aliyu
Habibu Gwarzo, tare da Habibu Sani da suka kudiri wayar da kan mutane domin
wayar da kan mutane akan ayyukan raya
Kasa da ake yi na ci gaba da kuma ci
gaban tattalin arziki. Sun jaddada cewa
duk talakan da bai zabi Buhari ba bai san
ciwon kansa ba. Matasan sun yi wannan batu ne a wani shiri da suka kaddamar
mai suna 'DON TUWON GOBE'
"Dalilin da ya sa muka kudiri bincike akan
ayyukan Buhari saboda sukar sa da ake yi
ya fi aiki Kudu akan Arewa. Baba wata
jiha daya da Buhari ya ware ita kadai ya ke mata aiki, Buhari Najeriya ya ke yi wa
aiki ba jiha ba.
Amma ance titunan da ya ke yi a Kudu
babu irinsu a Arewa? Idan ka duba
titunan da ake magana a da muka yi
bincike a record sun ba da titi 365 wanda 121 gado su aka yi daga gwamnatin baya,
ragowar ne sabbi, kuma kowane idan aka
duba ci gaban Najeriya ne ba na wata
jiha kadai ba.
Ko titunan da ake yi a Kudu mutanen
Arewa ake taimakawa. Saboda kusan kaso 80 na kayan da muke amfani da su
daga Kudu ake kawo mana. Kuma ba
mutum daya ne zai amfana da titunan ba,
zai taimaka wajen ci gaban kasa da
tattalin arziki. Sannan babu wata jiha da
Buhari bai ba wa mukamai sama da goma ba. Shugaban kasa ba shugaban
Kano ba ne ko Shugaban Kaduna ko
Jigawa Shugaban Najeriya ne, ayyukan da
ya ke don kasa ya ke yi ba don jiha ba.
Me ya sa masu fadin maganar ba sa sukar
cewa an yi gidan wuta a Mambila ba a yi a Ogun ba? Me ya sa ba a sukar janyo
bututun mai daga Nijar zuwa Kaduna ba?
A baya Naira miliyan uku ta ke sa wa a
asusun jarabawar Jamb, amma yanzu a
lokacin Buhari Naira Biliyan Takwas aka
samu. PDP ta ce duk jihar da ta ke da mai ita za ta rike abinta sai dai su rika bayar
da haraji, kenan wadanda ba su da mai
bara ake so su yi?
Kwanan nan Buhari ya biya ma'aikatan
Nigerian Airways wanda shekara sama
sama da goma sha sun kasa biya. A baya wutar lantarki megawas 4,000 ne amma
yanzu megawas 7,000 ne da mu.
Najeriya ce a gaban Buhari ba tara dukiya
ba, bai zama rariya da dukiyar kasa za ta
zurare ba. Dole mu fahimtar da mutane
su yi kishin kasa su ajiye kabilanci mu so juna, ba wai kawai a kwashe dukiyar
Kasa ba. Daga kin gaskiya sai bata,
jama'a su dubi abinda Buhari ya ke yi
tsakani da Allah
Mu yi kokarin fada da cima-zaune, abinda
Buhari ya fada gaskiya ne, dole mu tashi mu yi kishin kasa, mu yi amfani da ilimi
mu tashi mu jajirce mu nemawa kanmu
da kasar mu mutunci a idon duniya ta
hanyar da ya dace.
please Ku tura zuwa sauran Groups

No comments:
Write Comments