samu ci gaba da har ta yi fina-finai iri-iri,
wadanda yawanci na barkwanci da
soyayya ne, da kuma almara, wadanda
kalilan ne. Daga ciki akwai fim din ban-dariya na
Adam A. Zango, wato Dan Kuka a Birni da
fim din Ali Nuhu da ya yi shi shekara 18
baya kuma ya sake yinsa yanzu, Mujadala,
da dai sauransu. Kabiru Jammaje, wanda shi ne
musabbabin farfadowar sashen Ingilishi
a Kannywood, ya sake daukar nauyin
wani kasaitaccen fim din sarauta mai
suna In Search of the King. Da alamun fim din Nafisa Abdullahi, Yaki
a Soyayya, ma za a ji dadinsa, saboda
haka shekarar ta 2018 ta kayatar. Wadannan fina-finan da aka jero a kasa
su ne suka fi shahara da fice a wannan
shekarar, wacce ta zo dab da babban
zaben Najeriya wanda za a yi farkon
shekara mai zuwa. Ga shi siyasa ta kunno kai cikin
masana'antar ta Kannywood, har ma ake
ganin ta janyo rarrabuwar kawuna gami
da barazanar kara raba kan mambobin
masana'antar da ba a jima da sasanta su
ba - kodayake, wannan ba shi ne maudu'inmu yanzu ba. Fina-finan ba bisa daraja aka jera su ba: 1. Ruwan Dare Fim din, wanda daraktansa shi ne Yaseen
Auwal kuma ake ganin yana daya daga
cikin fina-finan Kannywood da suka fi
dacewa da yanayin da ake yanzu, yana
shagube ne cikin salon tsoratarwa ga
matasan da suka gama jami'a kuma suke raina duk wani aikin da ba na ofishi ba. Aminu Sharif, wato Momoh, da Sadiq Sani
Sadiq wasu mutane ne da suke son yin
kudi ko ta wane hali kuma masu tsananin
buri ne, wadanda sun gama digirinsu na
farko a fannin Akanta da Tattalin Arziki. Abokinsu kuwa, wanda shi ma ya gama
jami'ar, Baballe Hayatu, ba irin salonsu ya
dauko ba. Saboda haka, daga karshe sai ya samu
nasara. Su kuma wadancan biyu daga karshe sun
koyi darasi sannan suka yi nadama. Fim din ya yi matukar haduwa saboda
yadda jigonsa yake da alaka da wannan
zamanin. Kuma 'yan wasan, wadanda aka ambaci
sunayensu a sama da ma wadanda ba a
ambata ba, sun yi kokari sosai. Za a iya kau da kai daga 'yan kura-kuran
cikin fim din - irin su ambatar Yugoslavia
a matsayin kasa, kura-kuran nahawun
Turancin Ingilishi, da sauransu. 2. Rabi'atu Rabi'atu, wanda Aminu S. Bono ya yi
darakta, an shirya shi ne kwata-kwata a
gidaje guda uku; kuma yana nuna irin
hadarin da 'yar aikin gida ke shiga a
gidan da take aiki. Maryam Yahaya, wacce ta fito a matsayin
ita ce Rabi'atu, takan yi duk aikace-
aikacen babban gidan Alhaji Rabiu
Rikadawa, yayin da matarsa, Hadiza
Muhammad, kuwa ke zuwa wajen aiki;
'ya'yansa hudu kuma makaranta suke zuwa. Rabi'atu dai yarinya ce mai yarinta kuma
kamammiya, wacce gidansu ba masu
karfi ba ne. Saboda haka kowa a cikin gidan da take
aiki sonta yake yi, har ma manyan 'ya'yan
gidan guda biyu suke takara da juna
wajen samun karbuwar soyayya a
wajenta. Sai dai ba ta amince da su ba, tana mai
jaddada musu cewa sun wuce ajinta. Sai dai duk da haka ba wanda ya hakura
a cikinsu. Ana haka, kwatsam sai wata rana Alhaji
ya zo gidan ya same ta ita kadai har ya yi
lalata da ita. Daga bisani, sai matar Alhaji ta gano
Rabi'atu fa ta samu juna-biyu sakamakon
lalata da Alhaji ya yi da ita. Aka yi ta gumurzu dai har zuwa karshe. Fim din bai ci kudi ba, amma ya yi
matukar dacewa da yanayin da ake ciki
yanzu. Sannan, labarin ya yi kama da zahiri
kuma daraktan da mataimakansa da
kuma 'yan wasan, wadanda ba
shahararru ba ne, sun yi aiki da basira
sosai. Babu rawa da waka a ciki. Ba ma wannan ba, karshen fim din ya
kayatar. 3. Fuska Biyu Fuska Biyu yana nusarwa ne game da
yadda wasu iyaye ke saurin aurar da
'ya'yayensu mata ba tare da bincike kan
mazajen da za su aurar wa ba. Fim din yana ba da labari ne na wani
madugun masu garkuwa da mutane,
Adam A. Zango, wanda da rana yake
bayyana a matsayin mai sayar da kifi. Amal, wata kamilalliyar yarinya, wacce
'yan uwanta ba masu karfi ba ne, takan
sayar da abinci a gefen teburin da Zango
ke ikirarin yana sayar da kifi. A haka sai suka fara soyayya. Irin abin duniya da yake ba ta ya sa
mahaifiyarta take jin akwai lauje cikin
nadi. Amma mahaifinta kuma ya dage cewa
'yarsa fa ta samu mijin aure. Sai kuma da lokaci ya kure sannan
mahaifin ya fahimci kuskurensa. Fim din akwai jan hankali cikinsa. Yana da amfani sosai a kalle shi. 4.Risala Sunan wannan fim, Risala, wata kalma ce
ta Larabci, wacce ke nufin "sako". Risala, wanda Abubakar S. Shehu ya yi
darakta, siffofin zamanin baya yake da
su. Gogaggen tauraron nan, Sadiq S. Sadiq
(Zakariyya), ya yi wata tafiya da nufin
neman mutumin da ya yi wa ba-daidai ba
don neman afuwa. Tafiya ce mai cike da karaskiya, masifu
da abubuwan al'ajabi. Abin bai tsaya a haka ba - sai da ya sake
haduwa da wata jarrabawa a wani gari
da ake kira Baihan, garin da mutumin
yake. Wannan mutumin ya yarda zai masa
afuwa amma sai in ya amince zai auri
'yarsa, wacce, a cewarsa, ta fi kowa muni
a garin kuma musaka ce. Sai Zakariyya ya amince amma ba cikin
son ransa ba. Ashe dai yarinyar nan ba haka take ba;
hasali ma, yarinyar matukar kyau ne da
ita. Bayan 'yan kura-kurai da fim din ke da su
kamar rashin takaita darussa da yake
koyarwa, da kuma ci-da-karfi wajen
aiwatar da wasu abubuwa, fim din ya
dauko tarihin haihuwar shahararren
malamin addinin Islaman nan ne, Abu Hanifa. Kodayake yawancin fina-finan
Kannywood kwaikwayo su ake yi daga
wani waje. Baya ga haka, sautin shirin ya dauku. 5. Hakki Kamar yadda ake fada, tsohuwar zuma
da ita ake magani. Sanannen kamfanin shirya fina-finai,
Iyantama, shi ya yi fim din Hakki yayin da
Hafizu Bello, kwararre a harkar, ya yi
darakta. Labari ne kan wani mai suna Jabir,
wanda jajirtaccen ma'aikaci ne kuma dan
gwagwarmaya a wani kamfanin fata. Ba a san shi da karba ko ba da cin hanci
ba. Ba tare da nuna fargaba ba, yake yaki da
rashin adalci da kuma rashin kyautawar
da hukumar kamfanin ke yi wa
ma'aikata. A bangare guda kuma, akwai labarin
wani gungun 'yan mata da suke janyo
mazaje cikin wani loko domin abokansu
na aikata miyagun laifuka su samu damar
fasowa don yi musu fashi. Har yanzu fim din a sinima kawai ake
samunsa. Ya kuma samu damar shiga sahun fina-
finai don samun lambar yabo. Ya samu karbuwa ne saboda irin sakon
da yake isarwa, wanda gaba daya ya sha
bamban da irin fina-finan Kannywood na
soyayya. Kuma ya dace da zamanin da ake ciki
musamman yayin da kungiyar kwadago
ke ta fama da gwamnati wajen ganin an
samu karin albashi. 6. Mariya Fim din Mariya, wanda Ali Nuhu ne
daraktansa, yana nuni ne kan yadda
lamarin auren 'ya mace yake a kasar
Hausa. Labari ne na Maryam Yahaya, wacce ta
fito a matsayin Mariya kuma ake
tuhumarta da kashe mijinta, Baba
Karkuzu, da abokinsa, Musa Maisana'a, ta
hanyar saka musu guba. Kafin a yi mata auren dole, tare da
Abdullahi (Umar M. Sharif) take soyayya. Ga shi tana da buri na karantar aikin
likita. Daga bisani sai aka gano ashe ba ita ta yi
kisan ba. Babban kuskure a cikin fim din shi ne
rashin fito da takamammun al'amura fili. Duk da haka, fim din ya dace da zamanin
da ake ciki yanzu. 'Yan wasa ma sun yi kokari. Maryam Yahaya, kamar yadda ta saba, ta
yi abin a-zo-a-gani. Wadanda suka fito hatsabibai ma kamar
su Garzali Miko, Baba Kurzuku, da
Alhassan Kwalle sun taka rawar gani. Tacewa da haskakawa da kuma kwalliya
a fim din suna da jan hankali. 7. Larai Ko Jummai Rikici tsakanin kishiyoyi ba bakon
maudu'i ba ne a Kannywood yayin da
nuna fada kan 'ya'yayen kishiyoyin kuwa
abu ne bako. Jummai (Amal Umar) da Larai (Maryam
Yahaya) 'yan uba ne. Yayin da mahaifiyar Jummai (Ladidi
Fagge) masifaffiya ce, ta Larai kuwa ba
haka take ba: shiru-shiru ce. Mijinsu (wato Bashir Nayaya) yana ta
hakuri da su dai. Kamar yadda ya saba faruwa a kauyuka,
kawai sai 'ya'yan baffanunsu (Abdul M.
Sharif da Garzali Miko) suka tsunduma
cikin soyayya da wadannan 'ya'yan Bashir
Nayayan. Da yake Garzali attajiri ne saboda a birni
yake aiki, Ladidi sai da ta yi kutun-kutun
ya auri 'yarta. Kwatsam sai abubuwa suka sauya: Abdul
ya zo ya fi Garzali kudi bayan ya bi shi sun
tafi birni tare. Sadiq N. Mafia ne daraktan fim din kuma
shi wannan fim ya kece sauran fina-finai
saboda dalilai da dama, duk da bai watsu
kamar sauran fina-finai ba saboda ba a
kashe masa kudi sosai ba. Fim ne da ke matukar nuna zahiri, wanda
za mu iya cewa shi ne zakara wajen nuna
ainihin rayuwar Hausawa a kauye da
kuma rashin jituwa kan "abin da bai taka
kara ya karya ba" da ke tsakanin kishiyoyi
a gidan mijinsu. 8. Taqaddama Fim ne da Ali Gumzak ne daraktansa
kuma labari ne na "abin da ya taba
faruwa da gaske" na wani sangartaccen
dan wani shahararren mai kudi, Hassanu
(Aminu Sharif). Duk lokacin da ya yi laifi aka kulle shi,
attajirin mahaifinsa, Alhaji Bilya (Ali
Nuhu), wanda yake kut-da-kut da 'yan
siyasa, kan ba da kudi domin a sake shi. Ga shi mahaifin ba ya karbar shawara ko
uzurin kowa. Sai dai Hassanu da mahaifin nasa
karshensu bai yi kyau ba bayan ya kashe
abokinsa, Salisu, a lokacin da suka yi
rigima a wani gidan rawa. Hassanu ya ja kunne wa dayan abokinsu,
Nura (Abba Almustapha), wanda aka yi
kisan a gabansa, cewa kar ya fada wa
kowa shi ma zai kashe shi. Sai dai Nura bai iya barin wannan
barazana a zuciyarsa ba, wanda hakan
shi ya tona asirin wanda ya yi kisar, wato
Hassanu. Fim din ya yi kokari wajen nuno yanayin
rayuwar manyan Najeriya. 'Yan wasan sun yi kokari. Shirin Ya koyar da darasi sosai, duk da
cewa "kayatarwa" da "koyar da darasi" a
lokaci guda abu ne da Kannywood ke
fama da shi. 9. Kawayen Amarya Fim ne da 2 Effect Empire wanda kuma
Yakubu Muhammad ya ba da umarni. Kuma fim ne da 2 Effect din suka saba yin
irinsa, wato mai kyale-kyale da kuma
tattaro manyan taurari. Labari ne na wani mai kudi, Alhaji
Abdulsalam, da ke da mata uku. Bai taba haihuwa ba. Saboda fargabar haka sai ya dauko wani
yaro ya mayar da shi a matsayin dansa. Daga baya ma sai matan nasa suka samu
juna biyu suka haihu. Uwar gidansa (Saratu Gidado, wato Daso)
kullum alfaharinta shi ne "ai mahaifinta
ne sanadin kudin Alhaji", saboda haka, ya
kamata komai nata da na danta ya zama
daban. 'Ya'yan Alhaji (wato Ali Nuhu da Sani
Danja da kuma Yakubu Muhammad) a
rana guda suka yi aure. Kamar yadda sunan fim din yake, haka
fim din ma yake tattare da cakwakiya da
kaceniya a yayi da bayan bikin auren,
wanda yawancin kwayayen amaren ke
janyowa. Duk da fim din na ban-dariya ne, amma
yana dauke da darrusa. Babban matsalarsa ita ce "sautin ADR",
wanda shi ne sake nadar murya don a
saka wa fim kafin watsa shi. Maganganun ba sa tafiya daidai da
motsin lebe a fim din. Haka dai babu abin da aka yi wa Daso
bayan ta kashe mutane har biyu. Fim ne da zai kayatar sosai. 10. Li'ani Ali Gumzak ne daraktan wannan fim din. Labari ne na wani mai suna Alhaji Sunusi
(Rabiu Rikadawa), wanda sam ya ki yarda
juna-biyun da matarsa ke da shi nasa ne. Hakan ya kai ga sun je gaban alkali sun yi
rantsuwa (Li'an). Dan da ta haifa, wanda shi ne Ali Nuhu, a
wajenta da mijin da ta aura ya girma. Sai dai daga baya alhaki ya bi Alhaji
Sunusi, wanda yake ganin kamar sakayya
ce daga Ubangiji sakamakon abin da ya yi
wa wannan matar tasa. Mata takwas ya aura, yayin da daya daga
cikinsu ta taba yunkurin kashe shi, amma
hakan bai yiwu ba. Sai da lokaci ya kure kafin ya gane
kuskurensa. Fim din ya hadu saboda irin maudu'in da
ke ciki, wanda ba a saba yin fim a kansa
ba. Masu shirya fim din da 'yan wasan duk
sun yi kokari sosai wajen saurin fito da
al'amura fili. Babu waka ko rawa a ciki. Akwai wasu 'yan al'amura na daban
wadanda su ma sun taimaka wajen isar
da ainihin sakon fim din...
Muna Fatan Allah yakara Basira Ameen
No comments:
Write Comments